Tattalin arzikin Najeriya ya kama hanyar mikewa a Gwamnatin Buhari
- Alkaluma sun nuna cewa tattalin arzikin Najeriya na kara habaka
- Kayan masarufi na rage tsada a Najeriya ba kamar a lokacin da ba
- Kudin kasar wajen Najeriya na kara yawa bayan tashin man fetur
Mun samu labari cewa alkaluma sun nuna cewa tattalin arzikin Najeriya zai habaka a shekarar bana. Hakan na zuwa ne bayan da Najeriya ta samu kan ta cikin radadin tattalin arziki kwanakin baya a Gwamnatin Shugaba Buhari.
Alkaluman da ke yawo na tattalin arzikin kasar nan sun nuna cewa za a samu cigaba wajen harkar tattali da karuwar jimillar kudin Kasa watau GDP. Bayan haka kuma darajar kudin kasar zai karu a kasuwa duk a wannan shekarar da aka shiga ta 2018.
KU KARANTA: Marasa zuwa Makaranta sun ragu a Gwamnatin Shugaba Buhari
Tattalin arzikin kasar ya habaka ne ta fannin raguwar tsadar kaya da kuma samun saukin kasuwanci yanzu haka. Abubuwa dai sun fara mikewa ne a Gwamnatin Shugaba Buhari bayan da aka kawo shirin ERPG da zai farfado da tattalin arzikin kasar kwanaki.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa kayan masarufi na rage kudi a Najeriya, haka kuma kudin kasar waje na cigaba da karuwa yanzu a asusu. Har wa yau darajar Dalar Amurka na raguwa yayin da Gwamnati ke sakin kudi na aikace-aikace a fadin kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng