Gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki sabbin malaman Sakandari 330

Gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki sabbin malaman Sakandari 330

- Gwamnatin jihar Jigawa ta daukin sabbin malaman makaranta guda 330

- Malaman da aka dauka za su koyar da darussan Turanci, Lissafi da kuma kimiyya ne a manyan makarantun sakandare

- Kwamishinan ilimi na Jihar, Hajiya Rabi Ishaq yaba wa Gwamnan jihar inda tace daukan aikin zai rage matsalar karancin malamai da jihar ke fama dashi

Gwamnatin Jihar Jigawa ta mika takardun daukan aiki ga sabbin malamai 330 da aka dauka aiki, malaman za su rika koyarwa ne a manyan ajujuwan sakandari a makarantu daban-daban a Jihar.

Kakakin ofishin shugaban ma'aikatan jihar, Alhaji Isma'il Ibrahim ne ya bayar da wannan sanarwan a ranar Juma'a a babban birnin jihar, Dutse.

Gwamnatin Jihar Jigawa ta dau sabbin malaman Sakandari 330

Gwamnatin Jihar Jigawa ta dau sabbin malaman Sakandari 330

A yayin da yake mika musu takardun daukan aikin a ranar Alhamis, Shugaban ma'aikata na Jihar, Alhaji Muhammad Inuwa ya bayyanawa cewa malaman da aka dauka za su koyar da darussan Turanci, Lissafi da sauran darussan kimiyya.

DUBA WANNAN: Daliban Jami'ar Jihar Osun sun yanke jiki sun fadi a cikin aji

Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta dauki ma'aikatan ne domin tsohe gibin malaman makaranta da jihar ke fama dashi a fannin na ilimi.

Tun da farko, Kwamishinan Ilimi na jihar, Hajiya Rabi Ishaq ta lura cewa wannan shine karo na farko da gwamnatin jihar ta dauki malamai sama da 300 a lokaci daya a ma'aikatar na ilimi.

Kwamishina ta yaba wa Gwamna Muhammad Badaru Abubakar inda ta ce daukan sabbin malaman zai rage yawan masu zaman kashe wando a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel