Nade-naden Shugaban Kasa Buhari sun bar baya da kura

Nade-naden Shugaban Kasa Buhari sun bar baya da kura

- Kwanan nan aka nada sabon Shugaban Hukumar NIA na tsaron kasa

- Ana zargin cewa ba ma asalin ‘dan Najeriya bane wanda aka nadan

- Ana cewa Ahmad Rufai ‘dan cikin gida ne tun can a Gwamnatin nan

- Ahmad Rufai ya taba zama mai ba Shugaban kasa Buhari shawara a da

A kwanan nan ne Shugaban kasa Buhari ya nada Ahmad Rufai Abubakar a matsayin Shugaban Hukumar tsaro na NIA. A baya dai an kori Shugaban Hukumar tsaro Amb. Ayo Oke bayan wata badakala da ta bayyana. Sai dai ana ta surutu game da sabon nadin Shugaban kasar.

Nade-naden Shugaban Kasa Buhari sun bar baya da kura

An zargi Shugaban Kasa Buhari da nada 'Dan Chad a gwamnatin sa

Ahmad Rufai yana cikin kwamitin da su ka binciki hukumar NIA bayan an sallami Ambasada Ayo Oke. Kafin nan kuma shi ne tafintan Shugaban kasar na harshen Faransanci da kuma Larabci. Sai dai ana zargin ba ma ‘Dan Najeriya bane asalin sa don yayi karatu ne a Kasar Chadi.

KU KARANTA: Buhari zai bar Najeriya zuwa wata kasar Afrika a Ranar Lahadi

Nade-naden Shugaban Kasa Buhari sun bar baya da kura

Daily Nigerian tace akwai kutun-kutun wajen nadin Shugaban NIA

Malam Ahmad Rufai yana amsa sunan Jihar Katsina inda ya fara aikin Gwamnati. Jaridar Daily Nigerian tace a Jihar Katsina ne aka yi masa wani zuku har ya kai mataki na 14 a aikin Gwamnati a dare daya. A lokacin Malam Ahmad Rufai yana aiki da Ambasada Zakari Ibrahim.

Ko ma dai menene mafi yawan manyan Jami’an tsaron kasar ‘Yan Arewa ne kuma wasun su sun fito ne daga Jihar Shugaban kasar ta Katsina. Hakan ta sa har wani Sanatan APC yace alfarma ake bi da nuna sanayya amma ba sanin aiki ba wajen ba da mukami a Gwamnatin nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel