Sunyi garkuwa da wata yarinya yar shekaru 14, sun nemi N100m kudin fansa
- Wasu masu garkuwa da mutane sun sace wata yarinya mai shekaru 14 a Katsina
- Sun nemi kudin fansa miliyan N100
- Hukumar 'yan sanda ba ta ce komai ba ya zuwa yanzu
Wasu 'yan ta'adda da suka yi garkuwa da wata yarinya mai shekaru 14 a jihar Katsina sun nemi miliyan N100 a matsayin kudin fansa. Mahaifin yarinyar, Alhaji Salisu Mai-Tiles, ya sanar da manema labarai hakan.
Masu garkuwa da mutanen sun sace yarinyar mai suna Khadijat ne a unguwar Sabuwar Abuja dake karamar hukumar Kankia.
DUBA WANNAN: Matasan Kungiyar Ohanaeze Ndigbo sun umurci makiyaya su fice daga yankin Kudu
A cewar mahaifin yarinyar, wadanda suka yi garkuwa da yarinyar sun kira shi a waya, sun nemi ya biya kudin fansa miliyan N30, yayin da yaji muryar wasu na yi wa mai maganar tuni cewar miliyan N100 ne ba miliyan N30 ba kamar yadda ya fada da farko.
Da yake bayanin yadda masu garkuwar suka sace Khadija, Mai-Tiles ya ce wasu mutane dauke da bindigu ne suka tsallako cikin gidansa da misalin karfe 1:30 na dare su ka dauke yarinyar bayan sun karbi kudi a hannunsa.
Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Katsina, DSP Gambo, bai yi wani karin haske ba a kan batun yayin da wakilin jaridar Daily Trust ya tuntube shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng