Martanin Fati Mohammed ga wasikar da wani Malam Datti Assalafiy ya aika mata

Martanin Fati Mohammed ga wasikar da wani Malam Datti Assalafiy ya aika mata

Fitacciyar tsohuwar jarumar nan ta dandalin shirya fina-finan Hausa Fati Muhammad ta maida maratani ga wasikar wani mutum mai suna mai suna Datti Assalafiy bayan ya yi korafin cewa tana biyewa masu kudi yan siyasa suna kwana dasu a gidan shakatawa.

Ga martanin da Fati ta yi a wasikarta ga Datti Assalafiy:

Na ga rubutunka a kaina sannan kuma nagode duk da dai ka daure mani kai a matsayinka na wanda kake ganin kanka a matsayin Ustazu amma maimakon kayi amfani da iliminka ka yi min nasiha sai ka bi son ranka, har kake fadin muna biyewa masu Kudi da ‘Yan siyasa suna kwana damu a Hotel Suna diban kudin talakawa su bamu.

Martanin Fati Mohammed ga wasikar da wani Malam Datti Assalafiy ya aika mata
Martanin Fati Mohammed ga wasikar da wani Malam Datti Assalafiy ya aika mata

Idan nasiha zaka yi ka bi hanyar da ya dace, nasan inda ace kanwarka ce ko ‘yarka ba zaka fada mata wadannan munanan kalamai da sunan Wa’azi ba amma idan cin mutumci ne yasa kayi wannan rubutun to ina jiran ci gabansa.

KU KARANTA KUMA: Zai yi matukar wahala Buhari ya sake nasarar zabe a 2019 - Sheikh Gumi

Kuma tunda Kace na tuba na nemi miji na aura to a shirye nake zan aure ka in dai har don Allah kake wannan Wa’azi naka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng