Hukumar sojin sama sun tarwatsa garejin motocin Boko Haram
- An gano garejin kanikancin motan yan Boko Haram
- Jirgin hukumar soji ya tarwatsa garejin tare da kashe wadanda ke ciki
Hukumar sojin saman Najeriya ta ce ta sau nasaran ragargazan shagon kanikancin motan Boko Haram a Sambisa.
Kakakin hukumar, AVM Olatokunbo Adesanya, ya bayyana hakan ne a wata jawabi yau Laraba a Abuja.
Game da cewar Adesanya, kafin yanzu sun gano cewa motocin yan Boko Haram na ajiye a wurin.
“An shirya jirgin NAF domin gudanar da bincike a kan Boko Haram motocin da motocinsu da ke ajiye a wurin wanda ya bayyana shagon kanikancin ne.”
“Jirgin liken asirin ya gano cewa Babura, motoci har da kwamandansu na ajiye a inda aka tarwatsa.”
KU KARANTA: Bam ya tashi a Maiduguri, 12 sun rasu a harin
Kakakin ya ce an gay an Boko Haram da dama suna yawo a wurin.
Ya kara da cewa anyi ruwan bama-bamai wajen tarwatsa garejin tare da hallaka yan ta’addan da ke ciki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng