Yadda jami’an DSS suka kama gawurtaccen shugaban masu garkuwa da mutane, Don Waney - DSS

Yadda jami’an DSS suka kama gawurtaccen shugaban masu garkuwa da mutane, Don Waney - DSS

- Rundunar hukumar jami'an tsaro na DSS sun bayyana yadda suka kama Don Waney

- Hukumar SSS ta ce daun wani ne ya dauki nauyin kashe- kashen da akayi a ranar bukin sabuwar shekara a jihar Ribas

Wani babban jami’in rundunar hukumar DSS ya bayyana yadda suka gano gidan da gawurtaccen shugaban masu garkuwa da mutane, Don Waney yake boya a jihar Enugu.

Hukumar DSS ta zargi, Don Waney, da daukar nauyin kashe mutane 23 a cikin wanin coci a ranar bukin shiga sabuwar shekara a karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni dake jihar Ribas.

Babban jami’in yace nasarar da jami’an tsaro suka samu wajen attisayen da yayi sanadiyar kashe, Done Waney, ya tsayar da cigaba da zubar da jini a jihar.

Yadda jami’an DSS suka kama gawurtaccen shugaban masu garkuwa da mutane, Don Waney - DSS
Yadda jami’an DSS suka kama gawurtaccen shugaban masu garkuwa da mutane, Don Waney - DSS

An yanke hukuncin kama, DoneWaney, ne bayan ya ba yaran sa umarnin kashe mutane a garin Omoku.

KU KARANTA : Al’amarin Najeriya bai fi karfin Buhari ba – Kungiyar BSO

“Jami’an tsaro sun ce, sun ji hirar da Waney yayi da daya daga cikin yaran sa a lokacin da yake basu umarnin kai wa makaratun, Asibitoci, kasuwanni da wuraren Ibada hari ta wayar tarho da na’urar su ta kama.

“Sun sanya ranar 8 ga watan Janairu a matsayin ranar da za su kai harin, muna samun wannan rahoto sai muka sanar da rundunar sojoji kasar akan al’amarin.

Wannan ya janyo hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da sojoji wajen gudanar da attisayen da yayi sanadiyar mutuwar mutuwar, Don Waney.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng