Hukumar 'yan sanda ta cafke barayin shanu da masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara

Hukumar 'yan sanda ta cafke barayin shanu da masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara

A yau laraba 17 ga watan Janairu, rundunar 'yan sanda ta jihar Zamfara ta cafke 'yan ta'adda biyar masu garkuwa da mutane tare da satar shanu, inda ta karɓo shanu 31 daga wurinsu.

Kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Muhammad Shehu, shine ya bayyana hakan a birnin Gusau, inda yace a yayin da jami'ai ke gudanar da sintiri a kauyen Dawa na masarautar Dansadau dake karamar hukumar Maru, sun yi kacibus da 'yan ta'adda uku masu garkuwa da mutane.

Jami'an tsaro a bakin aiki
Jami'an tsaro a bakin aiki

A cewarsa, an samu muggan makamai a tattare da wannan 'yan ta'adda da suka hadar da; babbar bindiga mai cin harsashai 16 da karamar bindiga ta tafi da gidanka tare da baburin hawa guda.

KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya za ta saki fursunoni 368 a jihar Kano

Ya ci gaba da cewa, hukumar ta kuma cafke ɓarayin shanu biyu da suka kai hari kauyen Tungar Dundu dake karamar hukumar Anka a ranar 15 ga watan Janairu, inda suka yi awon gaba da shanu 31 mallakin wani Alhaji Muhammad Dandare.

Kakakin 'yan sandan ya kuma umarci mazauna da su ci gaba da tallafa wa 'yan sanda da bayanai masu amfani don inganta tsaro wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng