Juyin mulkin 66: Jerin manyan da aka yi wa kisan gilla a rana mai kamar ta yau

Juyin mulkin 66: Jerin manyan da aka yi wa kisan gilla a rana mai kamar ta yau

Kun ji cewa a rana irin ta yau aka yi wa wasu Shugabannin Najeriya kisan gilla. Wanda hakan yayi sanadiyyar kifar da Gwamnatin fara hula karo na farko hara bin ya kai ga wasu juyin-juya-hali a kasar.

Akwai manyan Shugabannin kasar 4 da Matan su da masu aikin su ban da kuma manyan Sojojin Arewa da Jami'an 'Yan Sanda da dama da aka kashe a lokacin juyin mulkin Junairun 1966. Mun kawo jerin manyan wadanda aka kashe a lokacin:

Juyin mulkin 66: Jerin manyan da aka yi wa kisan gilla a rana mai kamar ta yau
Hotunan wadanda su ka taka rawar su a 1966

1. Abubakar Tafawa – Balewa

Emmanuel Ifeajuna ya kashe Firayim Ministan Najeriya a wancan lokacin a Babban Birnin Tarayya ne Legas domin kifar da Gwamnatin Kasar.

2. Ahmadu Bello Sardauna

A Jihar Kaduna dai Nzeogwu Chukwuma ya jagoranci kisar Firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello a gidan sa da kuma Mai dakin sa Hafsatu da wasu masu 'Yan aikin sa.

KU KARANTA: Yadda aka kashe Firimiyan Arewa Ahmadu Bello Sardauna

3. Ladoke Akintola

Shi ma dai Firimiyan Kasar Yarbawa watau Samuel Ladoke Akintola bai sha ba. Sai dai ba a samu damar kashe Firimiyan Kasar Inyamurai ba a lokacin.

4. Festus Okoti-Eboh

An kashe Ministan kudi na kasar Okotie-Eboh a Garin Legas wadanda Sojojin su ka zarga da satar dukiyar Gwamnati a lokacin yana ofis.

Bayan nan kuma an kashe wasu manyan Sojojin kasar da Jami’an ‘Yan Sanda wadanda su ka hada da: Samuel Ademulegun. Zakari Maimalari, Kur mohammed, Aboga Largerma, James Pam, Arthur Unegbe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng