Ana rikicin kujera a Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Kano

Ana rikicin kujera a Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Kano

- ‘Yan PDP a Jihar Kano sun shiga cikin rikicin shugabanci

- Ana shirin yin zaben sabon Shugaban Jam’iyya na Jihar

- Wani ‘Dan takara yace ana kokarin murde zaben da za ayi

Wani sabon rikicin siyasa na shirin rikita Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Kano har an nemi Shugabannin Jamiyyar na kasa su sa baki kamar yadda mu ka samu labari yanzu ba da dadewa ba daga Jaridar nan ta Daily Trust.

Ana rikicin kujera a Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Kano
Ibrahim Shekarau na PDP da Gwamna Ganduje kwanaki

Jam’iyyar ta PDP ta shiga rudu ne game da shirin zaben sabon Shugaban Jam’iyya na Jiha da za ayi kwanan nan. Za a yi zabe ne domin maye gurbin Alhaji Rabiu Dan Sharu da aka kora daga matsayin Shugaban Jam’iyyar a baya.

KU KARANTA: Shugaban Kasa Buhari ya bada wani sabon mukami

Yanzu haka Majiyar tamu tace mutane 5 ke neman kujerar ta Shugaban Jam’iyyar. Wadannan mutane sun hada da Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa, da Muhammad Rabi’u Sabo Bakin Zuwo da kuma Alhaji Aminu Sa’ad Beli.

Haka kuma akwai wani tsohon Kakakin Majalisar Jihar watau Gambo Sallau da ke harin kujerar sai Honarabul Abdullahi Maraya Barkum. Wasu ‘Yan Jam’iyyar sun ce ana kokarin nada Jibril Doguwa wanda kuma ba za su yarda ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng