Gwamnatin Sokoto ta fara bayar da horo ga malaman makaranta 3,374 a jihar

Gwamnatin Sokoto ta fara bayar da horo ga malaman makaranta 3,374 a jihar

- Gwamnatin jihar Sakkwato ta sanya dokar ta baci a fanin ilimi

- Hakan ne ya sa gwamnatin jihar ta shirya taron kara wa juna ilimi ga malaman makarantun firamare a jihar

- Gwamna Tambuwal ya ce hanya daya da za'a tabbatar yara suna samun ingantace ilimi shine koyar da malaman su dabarun koyar wa na zamani

A kokarin ta na farfado da darajar ilimi a jihar, Gwamnatin jihar Sokoto ta fara bayar da horo da malaman firamare 3,74 a jihar, a karkashin shirin za'a koyar da malamin sabbin dabarun koyarwa da karin ilimi.

A jawabin da ya yi a taron kadamar da shirin a Sokoto, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya sake jadada aniyar gwamnatin sa na ganin cewa yana bawa malaman ingantacen horo lokaci zuwa lokaci.

Gwamnatin Sokoto ta fara bayar da horo ga malaman makaranta 3,374 a jihar
Gwamnatin Sokoto ta fara bayar da horo ga malaman makaranta 3,374 a jihar

DUBA WANNAN: Mummunar hatsarin mota a hanyar Legas-Ibadan ya ci rayuka 10

Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan ilimin firamare da sakandare, Dacta Muhammad Jabbi Kilgori ya ce bayar da horon ya zama dole har idan ana bukatar bawa yaran da ke jihar ingantacen ilimi.

Tambuwal din ya ce gwamnatin sa za ta cigaba da bawa fanin ilimi muhimmanci domin tabbatar da samun ilimi mai ingantaci a jihar. Ya kuma yi kira ga malaman da suka hallarci taron su bayar da hadin kai domin amfana da shirin.

Shugaban hukumar ilimin firamare na jihar (SUBEB), Alhaji Bello Dancgadi ya mika godiyar sa ga gwamnatin jihar bisa goyon bayar da ta ke bayarwa wajen ganin shirin ya cin ma nasara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164