Jikokin Atiku zasu ta shi a hannun tsohuwar surukar sa bisa umarnin wata kotu

Jikokin Atiku zasu ta shi a hannun tsohuwar surukar sa bisa umarnin wata kotu

- Daga karshe dai kotu ta mika rikon yara ga mahaifiyar su, Fatima Bolori

- Tun bayan mutuwar auren su a 2007, Dan Atiku da tsohuwar matar sa Fatima Bolori suna ta rikici kan rikon yaran nasu

- Idan mai karatu bai manta ba, iyayen biyu sun taba katchame wa a makarantar diyar tasu inda kowa ke son tafiya da diyar

Bayan sun shafe lokaci mai tsawo kan batun rikon yara, Wata kotun majistare da ke Unguwar Tinubu na garin Legas ta mallaka wa tsohuwar matar dan Atiku Abubakar 'ya'yan su guda biyu.

Babban Majistare K.B Ayeye ne ya yanke hukuncin cewa yaran, Amirah Atiku mai shekaru 8 da kuma Aminu Atiku mai shekaru 7 za su taso hannun mahaifiyar su Fatima Bolori.

Jikokin Atiku zasu ta shi a hannun tsohuwar surukar sa bisa umarnin wata kotu
Jikokin Atiku zasu ta shi a hannun tsohuwar surukar sa bisa umarnin wata kotu

DUBA WANNAN: Matashi ya rasa ransa wajen gwajin maganin bindiga a Katsina

An daura auren iyayen yaran ne a garin Borno a shekarar 2007, sun kuma yi zaman aure na shekaru biyar kafin matsaloli suka sanya wata kotun shariah a garin Maiduguri ta raba auren a 2011.

Idan mai karatu bai manta ba, ma'auratan sun katchame a makarantar Greenwood da ke unguwar Parkview a Ikoyi da ke Legas inda mahaifiyar yaran ta je daukan diyar ta amma sai mahaifin ya zo da yan sanda masu masa rakiya ya hana ta daukar diyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164