An kusa gama gina katafaren Kamfanin Dangote da zai sharewa Najeriya hawaye

An kusa gama gina katafaren Kamfanin Dangote da zai sharewa Najeriya hawaye

- Aliko Dangote yana kokarin gina kamfanin da kaf babu irin sa

- Da zarar an kammalla aikin Najeriya ta rabu da matsalar mai

- Dangote zai kashe sama da Dala Biliyan $11 wajen babban aikin

A shekarar 2019 ake sa rai Aliko Dangote zai kammala gina kamfanin sa na tatar man fetur wanda a kaf Afrika babu irin sa a Legas.

An kusa gama gina katafaren Kamfanin Dangote da zai sharewa Najeriya hawaye
Kamfanin tace man Dangote zai iya aikin da NNPC ba zai iya ba

Kamfanin zai rika tace danyen mai har ganga 650,000 a kowace rana wanda zai kawo karshen shigo da man fetur da Najeriya ke yi daga kasar waje. Najeriya dai na kashe sama da Tiriliyan 2.5 kowace shekara wajen shigo da mai daga ketare.

KU KARANTA: Najeriya ta samu matsayi a Majalisar dinkin Duniya

Bayan fetur dai za kuma a samu gas da kuma takin zamani. Kamfanin dai katafare ne wanda kusan duk Duniya guda babu irin sa kamar yadda wani babban Ma’aikacin Kamfanin Mansur Ahmad ya bayyana. Najeriya za ta samu damar adana man fetur a kowace rana.

Najeriya dai za ta samu kudin shiga da Kamfanin haka nan kuma sa da mutane 100,000 za su samu aikin yi bayan kuma makudan kudin da Dangote zai samu na sama dala Biliynan 5 a kowace shekara. Masu ruwa da tsaki dai sun ce kamfanin zai taimakawa Najeriya matuka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng