Kamfanin wutar lantarki na KEDCO ya yi magana a kan karancin wutar lantarki
- Ana cigaba da fuskantar karancin samun wutar lantarki a jihohin Jigawa, Kano, da Katsina
- Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya bawa jama'ar jihohin hakuri
- Sun ce matsalar ba daga gare su ba ce
Hukumar kamfanin raba hasken wutar lantarki dake Kano (KEDCO) ya bawa abokan huldar sa dake jihohin Jigawa, Kano, da Katsina hakuri bisa karancin samun wutar lantarki a cikin 'yan kwanankin nan.
Kamfanin, ta bakin kakakinsa, Mohammed Kandi, ya ce matsalar ta samo asali ne tun daga cibiyar dake basu wutar lantarki ta kasa.
"Sau 6 cikin sati guda cibiyar samar da wutar lantarki ta samu matsala sakamakon gobara da aka samu a cibiyar samar da iskar gas domin amfanin injinan samar da wutar lantarki a jihar Legas," a cewar Kandi.
DUBA WANNAN: Farashin man fetur zai koma guda biyu
Ma'aikatar aiyuka, lantarki, da gidaje ta bayar da tabbacin gyara mazuraran iskar gas din da suka kone kuma kwanan nan wutar lantarki za ta wadata a ko ina.
Tun bayan kammala bukukuwan shigowar sabuwar shekara jihohin Jigawa, Kano, da Katsina, suka fada cikin matsalar karancin wutar lantarki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng