‘Yan Siyasan da ke harin kujerar Gwamnan Kaduna a zabe mai zuwa
Mun fahimci cewa a Jihar Kaduna, ‘Yan siyasa sun fara kokarin shiryawa zaben 2019. Yanzu haka akwai wasu manyan ‘Yan Jam’iyyar APC mai mulki da ke harin kujerar Gwamna Nasir El-Rufai. Akwai kuma wasu dabam da ke harin kujerar.
Kamar yadda majiyar mu ta bayyana mana, ‘Yan siyasar sun fara kokarin yadda za su kada Gwamnan da ke kan gadon mulki a zabe mai zuwa. Daga cikin masu wannan aiki akwai Sanatocin Jihar da kuma wani tsohon Dan Majalisar Jihar.
1. Sanata Sulaiman Othman Hunkuyi
Sanatan Kaduna ta Arewan yana cikin masu wannan shiri. Hunkuyi yana cikin wadanda su ka san siyasar Jihar Kaduna. Da farkon tafiya, Sanatan yana tare da Nasir El-Rufai kafin abubuwa su canza.
KU KARANTA: Gwamnan Zamfara Yari yayi zazzaga a Gwamnatin sa
2. Sanata Shehu Sani
Tun farko dai abubuwa su ka cabe tsakanin Sanatan na tsakiya da Gwamnan na Kaduna. Mu na tunani akwai hannun Sanatan wajen kokarin tika El-Rufai da kasa a 2019. Shehu Sani yana da Jamaa’a a kasa.
3. Honarabul Isa Ashiru
Tsohon ‘Dan Majalisar na Yankin Kudan yayi takarar kujerar Gwamna da El-Rufai a 2015. Kuma mu na tunani zai kara jarraba sa’a a 2019. Ashiru yana da kudin batarwa idan har zabe ya zo.
Dama can Jam'iyyar APC mai mulki na ta fama da matsaloli a Jihar ta Kaduna. Bayan wadannan kuma akwai wasu masu adawa da Gwamnan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng