Mai gida na ya fi so na a kan Mahaifiyar sa don haka ya sake ni – Wata ta fadawa Alkali

Mai gida na ya fi so na a kan Mahaifiyar sa don haka ya sake ni – Wata ta fadawa Alkali

- Wani mutumi yayi mamaki bayan da sahibar sa ta maka sa a Kotu

- Matar ta sa dai tace ya fifita ta a kan Uwar sa da ta kawo sa Duniya

- Tace ba ya iya taimakon Mahaifiyar sa don haka ta nemi saki a Kotu

Kwanan nan mu ka kuma samu wani labari a Kasar Saudiyya idan wata Budurwa ta nemi Kotu ta raba auren ta mijin ta bayan da ta gano Mijin ta ya cika kaunar ta fiye da har Mahaifiyar sa a Duniya.

Mai gida na ya fi so na a kan Mahaifiyar sa don haka ya sake ni – Wata ta fadawa Alkali
An nemi Alkali ya raba aure saboda soyayya tayi yawa

Wannan Mata mai shekaru 29 ta gigita Mai gidan ta bayan ta nemi a raba auren su saboda Mijin ta ya fifita ta ta a kan Mahaifiyar sa. Tace duk abin da ta ke so yana yi mata amma yana wulakanta Uwar sa don haka tace ba ta kaunar irin wannan namiji.

KU KARANTA: Aikin Shaidan ne inji wani Mutumi bayan ya bar Surukar sa da ciki

Yanzu haka dai Jaridar Saudi Gazette ba ta bayyana sunayen wadannan mutane ba. Wannan Mata tace duk wanda bai iya taimakawa Uwar sa ba abokin zama bane kuma zai yi iya yaudarar Matar sa ta aure a koyaushe don haka ta dauki wannan mataki.

An yabawa wannan mata a Kotu inda ake shar’ar da cewa ya kamata mutum ya fi daraja uwar sa kan kowa a Duniya. Wannan mai gida dai yayi mamaki ace mai dakin sa za ta bar sa duk da irin abin da yayi mata ya kauracewa dangin sa saboda ita.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng