Kai ne dan takararmu a 2019 – Kungiyar BYO ga Buhari, sunce dole ya sake takara

Kai ne dan takararmu a 2019 – Kungiyar BYO ga Buhari, sunce dole ya sake takara

- Kungiyar magoya bayan Buhari (BYO) ta yanke shawaran tsayar da shugaban kasa a madadin dan takaranta a 2019

- Kungiyar tace ta yanke shawarar ne bayan ta binciki ayyukan shugaba Buhari cikin shekaru biyu da suka gabata

- Kungiyar ta bayyana shawararta a birnin Mukurdi, jihar Benue, bayan saduwa da mambobinta

Kungiyar matasa magoya bayan Buhari (BYO) ta bayyana shugaba Muhammadu Buhari a madadin dan takaranta a 2019 kamar yanda ta bukace shi da ya sake neman zabe don inganta nasarori da ya kafa a gwamnatinsa.

A shawarar kungiyar wacce jaridar Vanguard ta wallafa, a karshen taron wakilai na kasa da aka yi a Makurdi, jihar Benue, kungiyar, ta bakin shugabanta na kasa, kwamred Yusuf Nlado, yace mambobinta sun bayyana shawarar ne bayan bincike kan nasarorin shugaba Buhari cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata.

Daga cikin shawarwarin, “Shahararru daga cikin nasarorin sun hada da yaki da rashawa, yaki da ta’addanci, kafa asusus guda daya ga kowace hukuma ta kasa, shirin amfanar da al’umma da Kwastom da shirin hukumar kudin shiga ta kasa da sauransu.”

Kai ne dan takararmu a 2019 – Kungiyar BYO ga Buhari, sunce dole ya sake takara
Kai ne dan takararmu a 2019 – Kungiyar BYO ga Buhari, sunce dole ya sake takara

Babban sakataren shirye-shirye na kungiyar BYO, Terhide Utaan, ya cigaba da cewa: “A halin yanzu bamu da wani zabi bisa shugaba Buhari wanda manufofinsa, ba tare da gardama ba, ya daura kasarmu kan hanyar cigaba.

KU KARANTA KUMA: Bazaku iya kayar da Buhari a 2019 ba – Tsohon kakakin PDP ga jam’iyyar adawa

“Lallai ne yau mutuncin kasarmu ta inganta a idon duniya kuma Najeriya ta soma dawowa da alfarmarta taron kasashe sanadiyan gwamnati da shugaba Buhari ke jagoranta."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng