Dogara ya tallafawa kananan 'yan kasuwa a Bauchi
- Kakakin majalisar wakilai ya taka rawar gani a rayuwar yan kasuwan jihar Bauchi
- Ya tallafa wa masu kananan karfi da kudaden habbaka kasuwancinsu
- Ya kai ziyarar ne tare da uwargidansa da dan majalisa mai wakiltar mazabar Misau/Dambam
Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya kai ziyarar ban girma kasuwannin wasu garuruwa da kauyaku da ke cikin jihar Bauchi.
Ya kuma hadu da kananan 'yan kasuwa da masu sana'o'in hannu tare da bayar da tallafin kudade ga masu kananan karfi domin su bunkasa kasuwancinsu.
Shugaban majalisar wakilan dai ya ziyarci kasuwannin kauyakun Zwall, Burgel, Kagadaman Dass, Maraban Liman Katagum da kuma kasuwar Kadagi da ke kan hanyar Bauchi zuwa Tafawa Balewa.
KU KARANTA KUMA: Shugaban matasa ya kaddamar da goyon bayansa ga takarar Atiku
Har ila yau uwargidansa, Gimbiya Dogara da dan majalisar dokoki ta jihar mai wakiltar mazabar Misau/Dambam, Ahmed Yerima ne suka mara masa baya a lokacin ziyarar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng