Yana da kyau a yi bikin murnar haihuwa Annabi Isa – Sheikh Abduljabbar Kabara
– Shehin Kadiriyya Abduljabbar yayi magana game da bikin Kirismeti
– Sheikh Jabbar Kabara yace Musulmai sun fi kusa da Annabi Isa AS
– Malamin ya bayyana wannan ne wajen wani karatu a Ranar Juma’a
Za ku ji cewa wani babban Shehin Tarikar Kadiriyya a cikin Kasar nan Abduljabbar Kabara yayi fatawa game da Kirismetin Kirismeti da mabiya addinin Nasara su ke yi a mafi yawancin fadin Duniya.
Sheikh Abduljabbar Muhammad Nasiru Kabara ya bayyana cewa ya halatta Musulmai su rika bikin ranar haihuwar Annabi Isa AS. Shehin ya bayyana haka ne bayan da aka yi masa tambaya wannan a wajen wani karatun sa na wannan makon.
KU KARANTA: Gemu ba ya hana karatu: Obasanjo ya kammala karatun zama Dakta
Babban Malamin Darikar kuma ‘Dan gidan Sheikh Nasiru Kabara ya fadawa Almajiran sa cewa sun fi Nasara kusa da Yesu don haka ya dace su rika murna da ranar haihuwar sa. Wasu dai Malaman ba su sallama da wannan lamari ba a Musulunci.
Jaridar nan ta Mikiya ta kawo wannan labari inda kuma tace an taba yi wa Marigayi Sheikh Abubakar Gumi wannan tambaya a lokacin rayuwar sa. Babban Malamin yace wajibi ne Musulamai su raya dare a wannan rana na bikin Kitismeti da ibada.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng