Shugaba Buhari ya tura sakon godiya na musamman ga Gwamna Ganduje bisa kyakkyawan tarba da ya samu a Kano (hoto)

Shugaba Buhari ya tura sakon godiya na musamman ga Gwamna Ganduje bisa kyakkyawan tarba da ya samu a Kano (hoto)

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikawa Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje wasikar godiya tare da jinjina kan irin kyakkyawar tarba da ya samu a yayinda ya kai ziyarar aiki jihar Kano.

Wasikar ta kasance na farko da shugaban kasar ya taba aikawa wani gwamna bayan ya kai ziyara jiharsa. Sannan kuma tana kunshe da zantuttuka masu nuna jin dadi akan kyakkyawan tarba da akayi masa a jihar.

Har ila yau wasikar na kunshe da irin gagarumar nasarar da gwamna Ganduje ya samu wajen kammala ayyuka a jiharsa.

Har ila yau, Shugaba Buhari ya nuna matukar jindadin sa bisa yadda Gwamna Ganduje ya kammala aiyukan gwamnatocin baya da kuma nasa, inda yake nuni da cewa tabbas gwamnati abar dorawa ce, daga inda na baya suka tsaya, batare da sa san zuciya a ciki ba, domin ci gaban al'umma.

KU KARANTA KUMA: Atiku na wasa da damar siyasarsa ta karshe – Babafemi Ojudu

Bayan wannan kalamai masu sanyaya zuciya, Shugaba Buhari ya nuna matukar farin cikin sa da wannan irin karramawa da ya samu daga al'ummar mutanen Kano da kuma Gwamnatin Ganduje, wanda wannan ta sa shugaban ya rattaba hannu akan wasu manya manyan aiyukan raya kasa da Kano zata amfana da su. Duk aiyukan nan, su na cikin kadan daga koken da Gwamna Ganduje yayi wa Shugaba Buhari, yayin ziyarar sa Jihar Kano.

Ga hoton wasikar a kasa:

Shugaba Buhari ya tura sakon godiya na musamman ga Gwamna Ganduje bisa kyakkyawan tarba da ya samu a Kano
Shugaba Buhari ya tura sakon godiya na musamman ga Gwamna Ganduje bisa kyakkyawan tarba da ya samu a Kano

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng