Hotuna: Aisha Buhari tare da Matan Gwamnonin Arewa 19 sun hallarci taron bada tallafi a Katsina
Uwargidan Shugaban Kasar Najeriya, Hajiya Ai'sha Buhari ta ziyarci garin Daura da ke Jihar Katsina domin hallartan taron bada tallafi ga al'umma maza da mata daga kowanne lungu da sako na Jihar.
Taron ya samu hallartan matan gwamnonin Arewa 19 daga sassa daban-daban na kasar nan. Kayyakin da aka baiwa al'umma sun hada da babura masu kafa 3, Kekunan dinki, Injinan markade, Injinan kadin Taliya, Buhunan fulawa da sauran su.
Uwargidan Shugaban kasar tayi kira ga al'umman da suka amfana da tallafin suyi amfani da kayyakin ta hanyoyin da suka dace domin tallafawa kansu har ma da iyalansu.
Al'umman kuma sun mika godiya da fatan Alheri da Uwargidan Shugaban kasan da sauran matan gwamnonin 19.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng