Jerusalem: Shugaban Kasar Turkiyya Erdogan yayi kaca-kaca da Trump
– Shugaba Donald Trump ya maida Jerusalem babban Birnin Israila
– Trump ya dauke Jakadancin Kasar Amurka daga Garin Tel-Aviv
– Shugaba Erdogan yace ba za su yarda da wannan danyen mataki ba
Mun ji cewa Shugaban Kasar Turkiyya Recap Erdogan yayi kaca-kaca da takwaran sa na Kasar Amurka Donald Trump na maida Garin Jeruslam babban birnin Kasar Israila a makon nan. Erdogan yace hakan neman tada wutan rikici ne da kuma cin fuska.
Trump ya kara kawo sabon rikici inda ya maida Garin Jerusalem a matsayin babban Birnin Kasar Israila, wannan ya fusata Kasashen Musulmai yayin da sauran Kasashen Duniya su ka yi ta yabawa wannan mataki da Shugaban na Amurka ya dauka.
KU KARANTA: An yi yunkurin tsige Shugaban Kasar Amurka Trump
Recap Erdogan a wani jawabi da yayi cikin fushi yayi barazanar cewa a matsayin sa na Shugaban Kungiyar kasashen Musulunci watau OIC zai tara Shugabannin Duniya a Birnin Istanbul cikin kwanaki 5 zuwa 10 domin daukar mataki game da batun.
Erdogan yayi kaca-kaca da Trump inda yace ya ji da matsalolin da ke gaban sa ba ya kara ta da wutar wata fitinar ba. Har wa yau Shugaban na Turkiyya ya koka da yadda ake yi wa Bayin Allah cin kashi a Israila amma Shugaba Netanyahu ya gaza komai.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng