Yaƙi a kasar Yaman: Yan Shi’a sun kashe tsohon shugaban ƙasar Yaman
Tsohon shugaban kasar Yaman, Ali Abdallah Saleh ya gamu da ajalinsa a hannun tsofaffin abokan su, mayakan kungiyar yan Shi’ar Houthi da aka dade ana fafatawa da su a kasar.
Shuwagabannin jam’iyyar marigayi Saleh ne suka sanar da mutuwar shugaban nasu, inda suka bayyana cewa an kashe shi ne a garin Sana’a, kamar yadda BBC ta ruwaito.
KU KARANTA: An cigaba da cacar baki, nuna yatsa da murza gashin baki tsakanin Jonathan da gwamnan Borno
An kashe Saleh ne sakamakon wani sabon rikici daya balle a ranar Larabar data gabata tsakanin bangarensa da kungiyar yan Shi’a, wanda a baya tare suke yaki, amma sai aka samu rabuwar kai a sanadiyyar rikici kan wani bangare ne zai karbi babban masallacin Sana’a.
A sakamakon wannan rikici an kashe sama da mutane 125, wanda hakan yayi sanadiyyar sauya abokai da Saleh yayi, inda ya nemi sulhuntawa da Sojojin Saudiyya, daga nan fa say an Shi’an suka fara zarginsa da juyin mulki.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Litinin 4 ga watan Disamba ne mayakan Shi’a suka dira garin da Saleh yake zama, inda suka mamaye unguwarsa, amma duk da haka sai ya ya samu ya fita, inda ya shiga mota tare da jama’ansa zasu gudu.
Sai dai mayakan sun bude ma motar dayake ciki wuta, har sai da suka kashe duk wanda ke cikin motar. Daga bisani kuma suka fitar da wani Bidiyo dake nuna gawar marigayi Saleh.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng