Kyawawan hotunan kafin aure na wasu ma’auratan Najeriya
Idan zukata biyu suka hadu, babu abun da ya rage sai jiran lokaci domin samun cikar buri wato kulla auratayya.
Ana shirin kulla alkhairi tsakanin wasu musulman Najeriya biyu, Injiniya Abdulmalik Y. Saleh da Fatima Madeeha. Kamar ko wasu mutane, ma’auratan biyu sun saki hotunan kafin auransu a daidai lokacin da suke shirin raya sunnar ma’aiki.
Kanwarsu, Salamatu Saleh ta tura ma Legit.ng hotunansu a shafin zumunta. Yayinda suke kirga yan kwanaki kalilan domin fara gudanar da shagalin bikin sannan kuma tuni sun fara samun sakonni na fatan alkhairi.
Mai shirin zama amarya Fatima wacce ke a matakin shekara ta uku a jami’ar ATBU Bauchi ta yi shard a ita cikin hotunan aurensu tare da mai shirin zama mijinta inda za’a gudanar da bikin a ranar 23 ga watan Disamba 2017.
KU KARANTA KUMA: Banga yadda za’ayi jam’iyyar PDP ta dauki Atiku da muhimmanci ba yanzu - Junaid
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng