Rub-da-ciki wajen barci yana matukar illa ga kashin gadon-baya Inji masana

Rub-da-ciki wajen barci yana matukar illa ga kashin gadon-baya Inji masana

- Ashe kwanciya ta rub-da-jiki yana da aibu ga lafiya dama

- Masana su ka gano wannan a wani bincike kwanan nan

- Dama dai can Musulunci ya hana kwanciya ta kan ciki

Wani bincike da masana su kayi ya bayyana masu cewa kwanciyar rub-da-ciki na da illa kwarai da gaske ga lafiyar mutum. A musulunci dai dama tun sama da sshekaru 1400 da su ka wuce Manzon Allah ya hana irin wannan kwanciya

Rub-da-ciki wajen barci yana matukar illa ga kashin gadon-baya Inji masana
Rub-da-ciki na hana minshari amma akwai illa

Kwanciya a kan ciki watau ruf-da-ciki kenan inji Hausawa na jawo matsala ga kashin baya. Kai asali ma idan aka dade ana kwanciya a kan ciki yana jawo babbar matsala har ta kai ma ga gocewa a kasusuwan bayan ‘Dan Adam.

KU KARANTA: Ana neman taimakon na wani mai cutar koda a Najeriya

Masana dai sun ce hakan ya fi illa ne ga mata masu juna biyu. Kwanciya ta cikin zai matsawa kashin baya don haka dole mata masu ciki su kiyaye. Dama dai zai yi wahala mai tsohon ciki ta iya kwanciya a kan cikin na ta.

Bincike ya nuna cewa nauyin mutum yana tsakanin wuyar sa ne don haka kwanciya a kan cika na iya jawo jijiyoyi su matsu haka kuma zai yi wahala gadon bayan mutum ya mike daidai idan ya kwanta ta haka wajen barci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel