A daina wanke gaba da sabulun kau da cutar fata – Likita

A daina wanke gaba da sabulun kau da cutar fata – Likita

Wata likita mai kula da lafiyar yara kanana Juliet Ochi ta gargadi iyaye mata da ma’aikatan kiwon lafiya da su guji yin amfani da sabulun da ke kau da cutar fata wato ‘Medicated Soap’ wajen wanke al’auran mata.

A cewar Juliet aikata hakan na kashe wasu kwayoyin ‘Bacteria’ wanda ke kare al’auran mace daga kamuwa da cututtuka da kan yi wa gaban mace illa.

“Tun farko anyi wannan sabulun ne domin kawar da cutukan dake kama fatar mutum ne amma ba don wanke al’auran mace ba.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya fasa zuwa Kano

Ta ce kamata ya yi a dunga amfani da sabulun da ake kira ‘Toilet Soap’ domin banda tsaftace gaban mace da sabulun keyi zai kuma kare ababen dake samar da kariya ga al’auran mace.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng