Ali Nuhu ba Ubangida na bane, Uba na ne – Adam Zango

Ali Nuhu ba Ubangida na bane, Uba na ne – Adam Zango

- Adam A Zango ya bayyana irin dangantakar da ke tsakanin sa da jarimi Ali Nuhu

- Ali ba ubangida na bane, Ali Kaman Uba ne a gareni inji Zango

- Zango ya rubuta budadiyar wasika zuwa ga makiyan sa aka bata sunan sa da su ke yi

Shahararren dan wasan kwakwaiyon Kannywood Adam A Zango ya bayyana irin dangantakar da ke tsakanin su da jarimi Ali Nuhu.

Adam A zango ya bayyana haka ne shafin sa na sa da zumunta na Instagram, inda ya karyata zargin da wasu su ke masa na cewa shi da Ali Nuhu ba sa ga maciji da juna.

Ali Nuhu ba Ubangida na bane, Uba na ne – Adam Zango

Ali Nuhu ba Ubangida na bane, Uba na ne – Adam Zango

Zango ya rubuta a shafin sa kamar haka.

KU KARANTA : Sabon Labari da dumi-duminsa: Ta Mugabe ta kare!

“Ali ba ubangida na bane, Ali Kaman Uba ne a gareni”.

A makon da ya gabata ne Zango ya rubuta budadiyar wasika zuwa ga makiyan sa akan kazafi da bata sunan da su ke yi masa a farfajiyar finafinan Hausa na Kannywood, inda ya ce yanzu ya kai makura duk Wanda ya ce masa cas zai ce masa kule.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel