Babban Malamin addini ya ba El-Rufai shawara game da sallamar Malamai

Babban Malamin addini ya ba El-Rufai shawara game da sallamar Malamai

- Gwamnan Kaduna ya dauki aniyar korar wasu Malamai a Kaduna

- Wadannan Malaman sun fadi jarrabawar da aka yi masu kwanaki

- Wani Shehin Malami a Jami’ar Ahmadu Bello yayi kira ga Gwamnan

Game da korar Malamai a Kaduna wani babban Malamin addinin addini Sheikh Saeed Yunus Zaria ya ba Gwamnatin Jihar shawara a hudubar sa ta Juma’a yau.

Babban Malamin addini ya ba El-Rufai shawara game da sallamar Malamai
An yi kira kira ga El-Rufai ya sake tunani kan Malamai

Babban Malamin na addini Dr. Saeed Yunus ya ba Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai shawara a mimbarin Masallacin ITN da ke Zariya game da shirin sallamar Malaman da su ka fadi jarrabawa da yake yi inda yace da fa tsohuwar zuma ake magani.

KU KARANTA: Fayose yace sam bai dace a sallami Ma’aikata har 20, 000 ba

Malamin yace tsofaffin Ma’aikatan sun fi yaran da ake shirin dauka sanin kan aiki. Malamin a hudubar sa ta Juma’a wanda yace ba kamfe yake yi ba ya kira Gwamnati ta ba Malamai hakkokin su sannan kuma a kara horar da su don kuwa yace sun san aiki. Malaman Makaranta: Da tsohuwar zuma ake magani Inji wani Malami ga Gwamnan

Limamin ya koka da yadda aka bar sha’anin ilmu ya tabarbare a Arewacin kasar yace an maida makarantun Gwamnati wajen yin kitso da saida atamfofi. Dr. Yunus yayi kira ga Talakawa su guji zage-zage da tsinewa Shugabanni yace kan su za ta fado.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng