Ministan Ilimi ya nemi Buhari ya kara yawan kudade a fannin ilimi

Ministan Ilimi ya nemi Buhari ya kara yawan kudade a fannin ilimi

- Ministar Ilimi Adamu Adamu ya shawarci shugaba Buhari ya kafa dokar tabaci a fannin ilimin Najeriya

- Adamu ya ce kudaden da aka ware wa fannin ilimin kasar a kasafin kudin shekara 2018 sun yi kadan

- Ministar ya ce har idan shugaban kasa yana son yaga canji sai ya kashe makdudan kudaden a fannin ilimin kasar

Ministar Ilimi Adamu Adamu ya yi kira da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa dokar tabaci a fannin ilimi Najeriya.

Adamu Adamu yayi wannan kira ne lokacin ne da ya halarci taron akan harkan ilimi da fadar shugaban kasa ta shirya wa ministoci ranar Litinin.

Minisatn, ya roki Shugabakasa Muhammadu Buhari ya kara maida hankali a fannin ilimi kasar, kamar yadda ya maida hankali sa kan matsalar rashin tsaro da kuma inganta tattalin arzikin kasar.

Ya kara da cewa a gaskiya kudaden da Najeriya ke kashewa a fannin ilimi ba sun yi kadan, ko wasu kananan kasashe a nahiyan Afrika sun fi mu kashe kudi a fannin ilimi.

Ministan Ilimi ya nemi Buhari ya kara yawan kudade a fannin ilimi
Ministan Ilimi ya nemi Buhari ya kara yawan kudade a fannin ilimi

Adamu ya ya yi gargadi da cewa gwamnatin tarayya sai ta kashe mkudan kudade a fannin ilimi idan tana son ta ga canji.

KU KARANTA : Seketaren gwamnatin tarayya ya ziyarci Alex Ekwueme a asibitin Landan

Da ya ci gaba da bayani, sai ministan ya ce idan har shugaban kasa na bukatar cika alkawurra 13 da ya daukar wa Najeriya lokacin yakin neman zabe a kan inganta ilimi, to tilas sai an rika kashe akalla naira tirilyan daya a duk shekara a fannin ilimi.

IShugabakasa Muhammadu Buhari ya ware ma fannin ilimin kasa naira bilyan 605.8 a kasafin kudi, wato kashi 6 bisa 100 kacal na kasasfin shekara 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng