Cikin Hotuna: Yadda wani mutum ya auri mata 3 a rana guda tare da sakin wasu a jihar Delta
Wani mutum mazauni kuma dan asalin jihar Delta da yayi shirin auren mata 6 a rana guda, ya watsar da 3 sakamakon rashin amincewar su. Wannan dattijon ya auri ragowar ukun a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba a garin Okpata na jihar.
Legit.ng ta ruwaito da sanadin wata Jeke Godwin Ejiroghene, inda ta bayyana a shafin ta na dandalin sada zumunta na facebook cewa, dattijon ya auri mata uku ne a garin Okpata dake karamar hukumar Udu ta jihar Delta.
KARANTA KUMA: Biyafara: Tayar da kayar baya na Kanu ta na jefa 'yan kabilar Ibo miliyan 11.6 cikin hatsari - Kalu
A yadda wannan dattijon ya tsara, ya so ya auri mata 6 ne a rana kuma lokaci guda, sai dai ragowar mata ukun sun ki amincewa da wannan tsari na shi.
Wannan Dattijon ya sha alwashin karo auren mata uku zuwa gaba domin ya cika wannan dogo buri na shi.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng