Lafiyar Mutum Jarinsa: Hanyoyi 6 na inganta lafiyar Dan Adam da kabewa ke yi
Da yawan mutane su kan dauki Kabewa a matsayin kayan abinci mai karawa miyar taushe yawa da dandano, sai dai Kabewa ta wuce matsayar da yawan al'umma suka ajiye ta.
Kabewa ta kushi sunadaran gina jiki na vitamins, minerals, Potassium, antioxidants, beta-carotene da kuma Fiber.
Wadannan sunadarai sukan taimaka wajen kawar da cututtukan jiki dan Adam wanda Legit.ng ta kawo muku kamar haka:
1. Hana kamuwa da cutar daji (Kansa)
2. Sunadaran vitamin C da beta-carotene na cikin kabewa su na inganta garkuwar jiki.
3. Kariya ga cututtukan fata ta dan Adam.
KARANTA KUMA: Yadda gwamnatin Buhari ke yaudarar jihar Akwa Ibom - Gwamna Udom
4. Kabewa tana inganta hanyoyin samar da sunadaran glucose a jikin dan Adam, wanda ke yakar cutar sukari.
5. Sunadaran vitamin C, vitamin E da beta-carotene suna karfafa lafiyar idanu na dan Adam.
6. Akwai kuma sunadaran fiber, potassium da kuma vitamin C dake kunshe a cikin Kabewa wadanda ke hana cututtukan hawan jini, ciwo da kuma bugawar zuciya.
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng