An bude gidan Rediyo mai zaman kanta na farko a jihar Bauchi, Albarka fm 97.5
- Tsohon shugaban gidan rediyon gwamnatin tarayya FRCN ya bude gidan rediyo mai zaman kanta na farko a jihar Bauchi
- Salihu Ladan ya sanya wa gidan Reidyo suna Albarka fm 97.5
- A garin Bauchi ne kadai za a iya kama tashar Albarka fm a yanzu inji Salihu
Salihu Ladan, tsohon shugaban gidan rediyo gwamantin tarayya FRCN ya bude gidan rediyo mai zaman kanta na farko a jihar Bauchi.
Salihu Ladan wanda ya kasance haifaffen jihar Bauchi ya bude gidan radiyo mai suna Albarka fm a cikin garin Bauchi
A ranar 1 ga wata Nawumba gidan rediyon Albarka fm 97.5 fm ta fara gwajin watsa shiye-shirye a cikin garin bauchi.
KU KARANTA : Sabon sekataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha yayi kaca kaca da tsigar ‘Your Excellency’ da ‘Executive Governor’
Da yake gwajin hakan Ladan Salihu ya amsa kira daga mutanen jihar domin sanin yadda suke kama tashan a wannan lokaci da aka fara gwajin watsa shirye-shirye daga tashar.
Salihu Ladan yace a garin Bauchi kadai za a iya kama gidan Rediyon Albarka fm 97.5 fm a yanzu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng