Lafiya Jari: Sirrika 7 dake tattare a jikin tsamiya
Tsamiya wani itace ne dake tattare da gardi da kuma tsami ta fuskar dandano, kuma ana amfani da ita a fannukan magunguna da kayan abinci. Tsamiya itacen bishiya ce mai tsaka-tsalle da ganye mai banƙaye da kuma 'ya'yan itace wanda ke tasowa a cikin kwaskwarima wanda yake da tsawo.
Bankade-bankade Legit.ng ta bankado bincike masana kiwon lafiya akan ire-iren sunadaran dake cikin tsamiya wadanda suka hadar da; vitamin C, vitamin E, vitamin B, Calcium, iron, Phosphorus, Potassium, Manganese da kuma Fiber.
Sakamakon wannan sunadarai da itace tsamiya ya kunsa, tana da yalwar arziki na kawar da cututtukan jikin dan Adam kamar haka:
1. Tana taimakawa wajen narkewar abinci tare da kawar da kwarnafi da tashin zuciya.
2. Tana kara sunadaran iron a jikin mutum, wanda ke taimakawa wajen warakar da ciwon kai, ciwon ciki, kasala da mutuwar jiki.
3. Sunadarin Thiamine dake cikin tsamiya yana taimakawa wajen bude kafofi da tashoshin jinin jiki.
4. Akwai sunadarin hydrocitric acid cikin tsamiya dake taimakawa wajen rage nauyin teba da nauyin jiki.
KARANTA KUMA: Wani musulmi ya kammala digiri na 3 a nazarin addinin Kiristanci
5. Tsamiya tana daidaita sunadarin insulin a jikin mutum, wanda yawan shi ko karancin sa ke sanya ciwon sukari.
6. Sakamakon maikon da tsamiya ke tattare da shi, tana taimakawa wajen hana kumburi na sassan jiki
7. Yalwar sunadarin vitamin C, yana inganta garkuwar jiki ta yadda jikin mutum zai yaki kananun cututtuka.
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng