Ummah Shehu ta fadi gaskiya cewa da tayi ‘Yan wasan yanzu sun fi na da gogewa – Mansurah Isah

Ummah Shehu ta fadi gaskiya cewa da tayi ‘Yan wasan yanzu sun fi na da gogewa – Mansurah Isah

- Mansurah Isah ta goyi bayan furucin Umma Shehu kan martanin da ta maida wa Ummi ZeeZee

- Umma Shehu tace yan wasan yanzu sun fi na baya gogewa

- Munsurah tace bata ga wani abin jayayya a kai ba

Tsohuwar Jaruma, kuma shahararriya a dandalin shirya fina-finan Hausa na Kannywood Mansurah Isah ta goyi bayan furucin Umma Shehu kan martanin da ta maida wa Ummi ZeeZee na cewa yan wasan yanu sun fi na baya gogewa.

Mansurah wace ta kasance mata ga wani jigo na masana’antar shirya fina-finan wato Sani Musa Danja ta fadi haka ne a wani hira da tayi da wakilin Premium Times a Abuja in da tace ita bata ga wani abin jayayya a kai ba.

Ummah Shehu ta fadi gaskiya cewa da tayi ‘Yan wasan yanzu sun fi na da gogewa – Mansurah Isah
Ummah Shehu ta fadi gaskiya cewa da tayi ‘Yan wasan yanzu sun fi na da gogewa – Mansurah Isah

A cewar ta: “ Idan ka duba yanzu jarumai na wannan zamani na samun cigaba, sannan kuma an samu cigaba a harkar kimiyya da fasaha da kuma kimiyyar yanar gizo. Ba za’a taba hada zamanin mu ba inda zaka wani fim din ma a wajen daukar sa ne ake gaya wa jarumi abin da zai yi ko fadi.

KU KARANTA KUMA: A kama tsohon shugaban fansho yanzu - Itse Sagay, Falana sun fada ma Buhari

"Yanzu kuwa za’a baka shi a rubuce kayi ta bita har zuwa ranar da za’a fara daukar fim din. Sannan akwai kwarewa yanzu ba kamar da ba. Saboda haka ba zaka ha daba.

“Wasu daga cikin wadanda muka yi zamani da su har yanzu suna damawa a fagen fim din amma dai ai kai kanka ka san ba za su iya hada kansu da masu tasowa ba sai dai su taka iya rawar ganin da zasu iya. Musamman mu mata da muke da kaiyadadden lokacin haskawa a rayuwa gaba dayan ta.”

Ta yabawa jaruman wannan lokaci da yin kira garesu da su mai da hankali a sana’ar domin ganin kannywood ya ci gaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng