Amfanin rake ga Dan Adam da za su ba za kayi sake ba

Amfanin rake ga Dan Adam da za su ba za kayi sake ba

- Rake da ka ke gani yana da matukar amfani ga jikin mutum

- Mai shan rake a kan kari zai zama yana da ruwa sosai a jikin sa

- Rake na maganin cututtuka da dama irin su kan sa da cutar koda

Masana sun tattaro amfanin rake don haka mu ka kawo kadan daga ciki. Rake na maganin cututtuka hanta da na koda da kuma cututtuka da ake kamuwa da su wajen kwanciya da kuma zazzabi har ma da cutar mura. Rake na kula da hawan jini da kuma sauran cutar jini.

1. Rake na kara kwaji

Saboda sukarin da yake cikin rake yana karawa mai shan sa kwanji a jiki. Wannan dai masana su ka gano haka.

2. Gyara jiki

Haka kuma rake na sa sassan jikin mutum irin su hanta da koda su rika aiki da kyau. Masu fama da larurar fitsari sun samu sauki.

KU KARANTA: Abin da ya faru da gawar wasu Fulani a Filato

3. Juna biyu

Ana so mai ciki ta rika shan rake domin ta samu sauki wajen haihuwa domin yana dauke da Sinadarin folic acid. Haka kuma yana da amfani ga da namiji.

4. Matsalar bawali

Wadanda ke fama da matsi a koda sai su nemi rake don kuwa yana da amfani a jiki saboda ruwan da ya ke shi.

5. Karfin kashi

Bayan nan kuma rake na kara karfin kashi saboda yana dauke da kalshium da wasu sinadaran irin su fasfaros.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng