Ko kusa baka cancanci shugabancin Najeriya ba - Tsohon hadimin Shekarau

Ko kusa baka cancanci shugabancin Najeriya ba - Tsohon hadimin Shekarau

A sakamakon mayar da martani da wani hadimi akan bincike da rubuce-rubuce na tsohon gwamnan jihar Kano Mallam Ibrahim Shekarau ya yi, ya bayyana cewa Mallam Shekarau bai cancanci shugabantar Najeriya ba sakamakon wasu dalilai da hujjoji da ya bayar.

Hadimin Mallam Hassan Sani Indabawa, ya mayar da martani kan wata wasika da gwamnan ya rubuta a ranar 22 ga watan Agusta na shekarar nan, inda Shekarau ya bayyana ra'ayin sa na neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019 mai gabatowa sakamakon kiranye da shawarwari da yake samu daga masoya na kungiyoyi da daidaikun mutane daban-daban a fadin kasar akan ya nemi takarar shugabanci Najeriya.

Sakamakon wannan kiraye-kirayen ne ya sanya tsohon gwamnan yanke hukuncin tsayawa takara, inda ya rubuta wasika yake neman shawarar tsohon hadimin na sa Indabawa, akan shima ya bayar da ta shi shawarar.

Legit.ng ta ruwaito daga wasikar hadimin da cewa, Shekarau ya nemi shawarar Mallam Hassan bisa ga amincewar sa da kuma tsammani na zai bayar da goyon baya sakamakon irin sanin da ya yi ma shi domin sun yi fadi tashi tare saboda haka ba bu abinda ba shi masaniya akan sa.

Ko kusa baka cancanci shugabancin Najeriya ba - Tsohon hadimin Shekarau
Ko kusa baka cancanci shugabancin Najeriya ba - Tsohon hadimin Shekarau

Hadimin ya bayyanawa tsohon gwamnan cewa, "zai yi mamakin irin batutuwa da zai zayyanawa duniya domin idan bai manta ba shi da kansa ya ce komai ka shuka to tabbas akwai ranar fuskantar sakamako a gaba, da wannan rikon na ga ya cancanci na bayar da shawara da kuma fadin gaskiya komai dacinta kuwa akan na yaudari kawunan mu."

"A sakamakon nasarorin da gwamnatin ka ta samu tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011, wanda watakila hakan ya sanya wasu jama'ar ke neman ka akan tsayawa takarar shugaban kasa. Gaskiya ne akwai nasarorin da wasu ma'aikatu, sassa da kuma cibiyoyi suka samu a lokacin gwamnatin ka, wanda kaso mai tsoka na musabbabin nasarorin ya zo ne sanadiyar shugabannin wannan ma'aikatu da cibiyoyi ba wai matsayin ka na gwamna ne ya janyo ba."

KARANTA KUMA: 'Ya'yan shugaba Buhari 2 sun yi tattaki tare da shi zuwa Kasar Turkiyya

"Ire-iren nasarori da kuma kwazo na ma'aikatun ruwa, shari'a, lafiya da makamantansu misalai ne a gare ka. Aikin gada da kuma ruwa na Tambuwa shine mafi koluwa wajen iren kwazo da gwamnatin ka ta yi, wanda shi kan shi sanadi ne daga irin gaskiya da kuma rikon amana ta Mallam Salihu Sagir Takai."

"Akwai ma'aikatar ilimi da hukumar jin dadin alhazai ta Kano wanda idan aka tuna baya abin kunya ne a gareka, sakamakon irin almubazzaranci da rashin kulawa da gwamnatin ka ta yi. A fari dai cibiyar ilimi ta SUBEB (State Basic Education Board) ta fara kwazo sai kuma daga bisani bayan ka nada macen 'yar siyasa gabannin karewar gwamnatin ka komai kuma ya tabarbare a cibiyar."

"A madadin ta kula da harkokin cibiyar da bige da kula da fuskantar wajen bata lokacin ta na yin kwalliya wanda hakan ya janyo tabarbarewa cibiyar."

"Wani abin takaici da kuma kasancewar sa abin kunya a gareka shine, irin almundahanar miliyoyin kudi da ka rinka yi, wanda a yanzu idan na tuna da almubazzarancin biyan Dalar Amurka 10, 000 na kowane kwana guda da kayi a Otel din Hilton na Kasar Saudiyya sai na ciza yatsa, ko kadan Najeriya ba ta bukatar almubazzarin shugaba makamancin ka."

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng