Rahma Sadau ta ce rayuwar 'ya mace a arewacin Najeriya akwai wahala
Rahma Sadau, 'yar im din Hausa da turanci, kuma mawakiya, ta yi tsokaci kan yadda mata ke shan wahala a arewa muddin suka ce sai sun kai wani munzali na matsayi a rayuwa, a yanki da ke riko kam-kam da addini da al'ada, da ra'ayoyin mazan jiya mutan da.
'Duk mace da tace zata yi wani hobbasa ko katabus da rayuwarta, a arewacin kasar nan, zata sha wahala sosai, kuma zata fuskanci tsangwam daga maza da ma al'umma' fadin Rahma Sadau, a hirarta da jaridar Thisday.
A dai cewar Rahman, tunda aka kore ta daga dandalin Kannywood, wai don ta yi waka da kiristan yaro ta rike hannunsa shikenan, sai duniya ta karbe ta, bayan nata na gida sun yada ta, sun kuma tsangwame ta.
DUBA WANNAN: Sanata Abaribe yace su da suka karbo belin Nnamdi Kanu sun shiga uku
A cewarta kuma sai harkoki ne ke kara bude mata ma, maimakon dakushe ta da al'umma suke son yi. Tace mata a arewacin Najeriya na fuskantar kalubale fiye da maza, a harkokin rayuwa gaba daya, ba ma wai a fim kadai ba.
A yanzu dai, sai da aka sake dawoda ita Kannywood sannan zancen ya lafa.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng