Allah sarki: A bar wata mahajjata daga Bauchi a Saudi Arabia

Allah sarki: A bar wata mahajjata daga Bauchi a Saudi Arabia

- Hukumar kula da Alhazai na jihar Bauchi ta ce ta bar wata mahajjata a Saudiyya saboda ta batar da fasfon ta

- Jami'an Najeriya a kasar mai tsarki suna kokarin samar wa mahajjatan sabon fasto don taimakawa mata dawo gida

- Hukumar ta ce an yi aikin Hajji na bana a cikin nasara da kwanciyar hankali

An bar wata mahajjata daga jihar Bauchi a Saudi Arabia bayan batar da fasfo na nata, in ji Alhaji Abdullahi Hardawa, babban sakataren hukumar kula da Alhazai shiyar jihar Bauchi.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Hardawa, wanda ya yi jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba a Bauchi, bayan zuwan jirgin karshe wanda ya dawo da mahajjatan jihar, ya bayyana cewa matan wanda ba a bayyana sunan ta ba ta na daga karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar.

"Dukan mahajjata sun dawo gida, sai dai wata mata wadda ta batar da fasfo na ta, mun bar ta a kasar Saudiyya saboda ta rashin Fasfo na tafiya" in ji shi.

Allah sarki: A bar wata mahajjata daga Bauchi a Saudi Arabia a kan batan fasfo
Masallacin Ka'aba

Hukumar ta bayyana ce jami'an Najeriya a kasar mai tsarki suna kokarin samar mata sabon fasto don taimakawa mahajjata dawo gida.

KU KARANTA: IMN ta gudanar da zanga zangar makoki na Ashura a fiye da garuruwa 60, suna neman a saki Sheikh Zakzaky (Hotuna)

Ya ce an yi aikin Hajji na bana a cikin nasara da kwanciyar hankali, ya dangana wannan ga cikakken goyon bayan gwamnatin jihar Bauchi.

Mai martaba sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Adamu, a cikin jawabinsa, ya yaba wa mahajjata daga Najeriya don nuna kyakkyawan hali a lokacin da suke ƙasar mai tsarki.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng