Jawaban majalisar dinkin duniya: Dalilin da yasa Buhari ya yi shiru akan IPOB
Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kame bakinsa akan rikice-rikicen masu fafutikar neman kafa yankin Biyafara (IPOB) cikin jawaban da gabatar a taron majalisar dinkin duniya domin baya son ta'azzarawa duniya abin.
'Yan Najeriya da dama sun yi tir da jawaban na Buhari akan cewar ya yi jawabai akan matsalolin wasu kasashen ya yi watsi da na kasar sa.
Mista Akeredolu wanda yana cikin tawagar shugaban kasar zuwa halartar taron na majalisar dinkin duniya, ya bayyanawa manema labarai a babban birnin New York na kasar Amurka cewa, rikicin IPOB lamari ne na cikin gida.
KARANTA KUMA: Muhimman Jawabai 5 na shugaba Muhammadu Buhari a taron majalisar dinkin duniya
A kalaman gwamnan, "tayar da kayar baya na kungiya IPOB ba abu ne da ya kai girman zayyana shi a majalisar dinkin duniya. Lamari wanda za a iya shawo kan sa a cikin gida Najeriya ba tare da ta'azzara shi a idanun duniya ba."
Gwamnan ya ce, shugaba Buhari ya yi jawabin wasu matsaloli da suke fuskantar kasar nan, kama daga tayar da zaune tsayen Boko Haram, cin hanci da rashawa da kuma karbo kudaden kasar nan da mamuguntantan da suka boye a kasashen ketare.
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng