Shin ko kun san, duk da cewa Amurka tafi kowa karfin tattalin arziki, haka kuma tafi kowa cin bashi a duniya? Duba nawa ake binta

Shin ko kun san, duk da cewa Amurka tafi kowa karfin tattalin arziki, haka kuma tafi kowa cin bashi a duniya? Duba nawa ake binta

Zafin nema baya kawo samu, Amurka duk da kudinta, da yawan arzikinta, tai kowa cin bashi a duniya, kuma kasashe masu kudi a hannu, masu tasowa, kamar su China da Japan suni kowa bata rancen kudin.

Dubi jerin kasashen duniya da suke bin kasar Amurka dumbin bashi, bashin dai da ake bin Amurkar, a ciki da wajen kasar, kusan dala tiriliyan 20 ne. Watau $19.8 Trillion dollars. Kwatankwacin naira quadrillion maitan kenan, malala gashin tunkiya.

Shin ko kun san, duk da cewa Amurka tafi kowa karfin tattalin arziki, haka kuma tafi kowa cin bashi a duniya? Duba nawa ake binta
Shin ko kun san, duk da cewa Amurka tafi kowa karfin tattalin arziki, haka kuma tafi kowa cin bashi a duniya? Duba nawa ake binta

1. Kasar China, tafi kowacce kasa bin Amurka bashi, da kusan tiriliyan daya na daloli, naira tiriliyan dari u da hamsin kenan.

2. Kasar Japan, ta uku a arziki a duniya bayan Amurkar da china, ita ma kusan tiriliyan daya take bi

3. Kasar Ireland, mai makwabtaka da Ingila, kwata tiriliyan take bin Amurka.

DUBA WANNAN: Mata sojoji da suka rasa miji, suna neman taimako da miji

4. Kasar Brazil ma dai kusan hakan take bin Amurkar, wato biliyan 250 na daloli.

5. Bashin cikin gida; kusan Tiliyan shida na daloli ake bin gwamnatin Amurka a cikin gida, wannan makudan kudade sun samo asali ne daga kudaden fansho, da na social security, da na bankuna.

A hasashe dai, wadannan kudade na iya karuwa har su ninku, daga nan zuwa shekarar 2030, kuma ga dukkan alamu babu dai ranar biya kam, musamman ganin kasar China na neman kwace ragamar karfin tattalin arziki a duniya, kambu da Amurkar ta rike kusan shekaru dari.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng