An sace uwa da 'yar ta a Sokoto, an tsince su a Kaduna
- An sace Mata mai suna Sa'adatu da 'yar ta mai suna Rumaisa'u bayan sun tafi gidan suna
- Daga hawar mu Keke Napep don dawowa gida muka sume, bamu tsinci kan mu ba sai a garin kafancha na Kaduna in ji 'yar
- A ranar Litini ne 4 ga watan Satumba aka sace wata mata, Sa'adatu Umar Abubakar mai shekaru 26 da 'yar ta, Rumaisa'u mai shekaru 7 a hanyar su ta zuwa gidan suna a Sokoto
Jaridar Daily Trust ta samu rahotan cewa tun kafin su kama hanya zuwa gidan sunan ta samu rashin natsuwa na wani abu zai iya faruwa. Mijinta, Abubakar Umar ya banyana yadda ta wayi gari fuskarta babu walwala kuma ta dauki tsawon lokaci kafin ta tafi gidan sunan.
''Shiru shiru har karfe 10 na yamma basu dawo ba. Na yi ta kiran wayan ta amma baya shiga. Daga nan ne sai nayi bincike a gidan sunan da gidan iyaye na da gidan iyayenta amma duk a banza. Ganin haka sai muka sanar a kafan yada labarai muka kuma bincika ofisoshin 'yan sanda da asibitoci'. Daga nan kuma sai muka dukufa da addu'a''. In ji mijin nata.
DUBA WANNAN: Shugabanin mulkin soji ne suka shuka kiyayya da gaba tsakanin yan Najeriya - Afe Babalola
Duk da dai Jaridar Daily Trust bata samu zantawa da uwar ba amma ta zanta da 'yar, Rumaisa'u a in da ta ce, ''mun hau keke napep mai dauke da mutum daya a gaba da mace daya a baya don dawowa gida. Muna shiga muka sume, bamu tsinci kan mu ba sai a wani daki mai dauke da mata guda 3, da alama daya daga cikin su ita ce mai dakin. Daga baya ne muka fahimci muna garin Kafachan ne a Kaduna''.
Rumaisa'u ta ci gaba da cewa, ''A rana na uku ne muka ji harbi daga wace a inda mu da sauran mutan gidan muka sheka waje. Sai wani soja ya kama hannun mahaifiya ta ya saka su cikin motan sojoji su ka kaimu gidan sa a inda kawu na ya zo ya dawo da mu Sokoto''.
Mijinta da 'yan uwa da abokan arziki da makota da mutanen gari sun yi farin ciki da mika godiyar su ga Allah da ya dawo da su lafiya.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng