Ke duniya ina zaki damu ne? Wani tsoho ya banka ma ƙaninsa wuta, ya ƙone ƙurmus

Ke duniya ina zaki damu ne? Wani tsoho ya banka ma ƙaninsa wuta, ya ƙone ƙurmus

- Wani tsohon ya hallaka dan uwansa ta hanyar babbaka shi da wuta

- Alkalin kotu ya bada umarnin garkame shi har sai an cigaba da sauraron shari'ar

Wani tsoho mai shekaru 60 a rayuwa Adegboyega Abiose ya banka ma kaninsa Olayinka wuta, inda yak one kurmus, wanda hakan yayi sanadiyyar garzayawarsa barzahu.

Jaridar Premium Times ta ruwaito wata karamar kotu ta aika da mutumin zuwa gidan maza a ranar Larab 6 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Yajin aikin dindindin: Mutanen jihar Kaduna sun yi magiya ga likitoci

Sai dai, da fari, dansanda mai kara, Sunday Fatola ya shaida ma kotu cewar tsohon Adegboyega Abiose ya aikata wannan mummunan laifi ne a ranar14 ga watan Agusta da misalin karfe 8 na safe.

Ke duniya ina zaki damu ne? Wani tsoho ya banka ma ƙaninsa wuta, ya ƙone ƙurmus
Tsoho ya banka ma ƙaninsa wuta, ya ƙone ƙurmus

Dansanda Fatola yace a wannan lokaci ne Adegboyega Abiose ya banka ma wata mota mallakin mamacin, kirar Toyota Camry wuta a yayin da mamacin ke cikin motar, inda dansandan yace wannan laifi ya ci karo da sashi na 316 na kundin hukunta manyan laifuka na jihar Oyo.

Bayan sauraron karar ne, sai alkali Abdullateef Adebisi ya dage sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Disamba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng