Dandalin Kannywood: Dukkan abun da kake bukatar ka sani game da mai zazzakar murya Ali Jita

Dandalin Kannywood: Dukkan abun da kake bukatar ka sani game da mai zazzakar murya Ali Jita

Yau kuma a dandalin namu na Kannywood, mu karkata ne wajen kawo maku tarihin mashahurin mawakin nan mai zazzakar murya na masana'antar fina-finan Hausa watau Aliyu Isa wanda aka fi sani da Ali Jita.

Shi dai Ali Jita an haife shi ne a unguwar gyadi-gyadi a cikin badalar Kano dake a Arewacin Najeriya sannan kuma ya yayi karatun sa na Firamare da kuma Sakandare duk a birnin Ikko na jihar Legas a wata makarantar sojoji,

Dandalin Kannywood: Dukkan abun da kake bukatar ka sani game da mai zazzakar murya Ali Jita
Dandalin Kannywood: Dukkan abun da kake bukatar ka sani game da mai zazzakar murya Ali Jita

Legit.ng ta samu kuma cewa daga baya ne sai mawakin ya kuma dawo jihar Kano inda ya kammala karatun sa na Difloma akan harkar mulki da kuma a fannin na'ura mai kwakwalwa duk dai a Kano din.

Mawakin haka zalika binciken mu ya samu cewa ya tsunduma a harkar wake-waken Hausa ne a cikin shekara na 2009 a inda kuma nan da nan ya samu karbuwa a zukatan al'umma sakamakon kwarewar sa da kuma zazzakar muryar sa.

Mawakin dai yanzu haka ya samu nasarori da dama inda ya lashe kyaututtuka masu tarin yawa sannan kuma ya fitar da kundin wakoki da yawa.

Ka wo yanzu dai lokacin hada wannan rahoton, mawakin yana da auren sa mata daya kuma Allah ya albarkace su da samun ya'ya biyu. Haka zalika babban masoyin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ne.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng