Adam A Zango ya zaburo da wani sabon salo a fim din ‘Gwaska’

Adam A Zango ya zaburo da wani sabon salo a fim din ‘Gwaska’

- Shararren dan wasan Kannywood ya zo da wani sabon tallar fina finai

- A Zango yayi amfani da Facebook, Twitter da sauransu wajen tallar fim

Fitaccen jarumin Kannywood din nan, Adam A Zango wanda ya shirya wani kayataccen fim a baya mai suna gwaska ya sake dawowa da cigaban Gwaska, amma da sabon salo.

Jaridar Rariya ta rwuaito tauraron na Kannywood, A Zango yayi amfani da wasu kafafen sadarwa wajen tallata finafinansa wanda ba’a saba ganinu ba a baya, da suka hada da Facebook, Twitter da Instagram.

KU KARANTA: Rikicin rusa kasuwan Owerri: An kashe dan shekara 10 – Mahaifinsa ya ba sojoji laifi

Masana harkar fina finai sun yaba da tsare tsaren da jarumin ya bi wajen tallata hajarsa, inda suka yi kira ga sauran yan Fim da suyi koyi da shi.

Adam A Zango ya zaburo da wani sabon salo a fim din ‘Gwaska’
Adam A Zango

A baya dama can Legit.ng ta ruwaito Adam Zango ya sha yin zafafan fina finai a baya wanda suka yi suna suka mamaye kasuwannin Arewa.

Kalli bidiyon anan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel