Karanta yadda shauƙin so ya kwashi wani saurayi inyamiri ya auri gyatuma mai shekaru 72
Wata gyatuma yar kasar Ingila ta kamu da soyayyar wani matashin dan kabilar Ibo wanda yayi mata magana a shafin sadarwa na Facebook, inda daga nan suka fara soyewa har lamarin ya kai ga aure.
Wannan mata mai suna Angela mai shekaru 72 tana da yaya da jikoki shidda, wanda karamin jikanta ma ya girmi saurayin nata da shekaru 6. Shi kuwa gogan nata wanda ta bayyana sunansa a matsayin CJ, matashine dan kabilar Ibo mai shekaru 27, wanda ya kammala digirinsa na farko.
KU KARANTA: Buhari ya gana da shuwagabannin jam’iyyun Najeriya a fadar shugaban ƙasa (Hotuna)
Sai dai Angela ta koka kan yadda jami’n ofishin jakadancin kasar Birtaniya suka hana sahibin nata izinin shiga kasar UK, duk da cewa tuni an daura musu aure a nan Najeriya, inda aka yi bikin a garin Owerri na jihar Imo.
Wani abin mamaki shine Angela ta tabbatar CJ ba kudinta yake nema ba kamar yadda ake samun wasu samarin suna auren tsofaffi domin kudinsu, musamman bayan ta fada masa ita fa tsohuwar direban tasi ce, kuma tayi ritaya, amma gogan nata yace ya ji, ya gani.
Da take bada labara ga majiyar Legit.ng, Angela tace “Bayan mutuwar aure na da wata 6, sai ga wani matashi kyakkyawa ya min magana a facebook, daga nan muka fara hira har muka saba, matsalata kadai shine na bashi tazarar shekaru 45, kuma a Najeriya yake zama.”
Angela tace ta samu goyon bayan yayanta su duka, a cikinsu akwai mai shekaru 50, 47 da kuma 43, kuma tace sun yi maraba da auren nata, sai dai basu biyo ta Najeriya ba don halartar bikin aurenta da CJ sakamakon a dan kankanin lokaci aka fada musu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Zaka iya auren yar wata kabila ta daban?
Asali: Legit.ng