Abu bai yi dadi ba: Ta kashe Mijin ta na aure

Abu bai yi dadi ba: Ta kashe Mijin ta na aure

- 'Yan Sanda sun damke wata mata ta kashe Mijin ta

- Wannan mummunan abu ya faru ne a cikin Garin Legas

- Dama dai an ce an saba samun matsala tsakanin su

Jami'an 'Yan Sanda sun damke wata mata mai shekara 42 ta kashe Mijin ta na aure a wata Unguwa a Garin Legas.

Abu bai yi dadi ba: Ta kashe Mijin ta na aure
Jami'an 'Yan Sandan Najeriya

Ana zargin Folashade Idoko da kashe Mijin ta a cikin gidan su. Jaridar Daily Post tace wannan mummunan abu ya faru ne a cikin Oto-Awori na Garin Legas. Marigayin dai Injiniya ne kuma tuni dai Jamia'an 'Yan Sanda su kayi ram da wannan mata.

KU KARANTA: An hurowa Shugaba Buhari wuta

Mai gidan hayan da Iyalin su ke yace matar wanda malamar asibiti ce ta dade su na samun matsala da Mijin na ta amma yana hakuri. Kuma dai akwai kishin-kishin din cewa kishin jaraba ne ya sa ta kashe Mijin na ta. Matar dai tace tsautsayi aka samu wuka ta fadi a jikin sa ya mutu.

Jami’an tsaro sun damke wani saurayi Ifeanyi Chukwu Maxwell Dike dauke da jikin wata yarinya da aka sace a makon jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kechi Okuchi tayi rai bayan hadarin jirgi

Asali: Legit.ng

Online view pixel