YANZUNNAN: Kani ga Danbaba Suntai ya rasu bayan binne yayansa

YANZUNNAN: Kani ga Danbaba Suntai ya rasu bayan binne yayansa

Kanin tsohon gwamnan jihar Taraba, marigayi Danbaba Danfulani Suntai ya rasu sa'o'i biyu bayan gama jana'izan tsohon gwamna Danbaba Suntai.

Babangida Suntai ya rasu ne a babban asibitin gwamnati da ke Abuja.

YANZUNNAN: Kani ga Danbaba Suntai ya rasu bayan binne yayansa
YANZUNNAN: Kani ga Danbaba Suntai ya rasu bayan binne yayansa

Ya rasu ne jim kadan da kammala jana'izan tsohon gwamna Danbaba Suntai wanda ya rasu a ranar 28 na watan Yulin wannan shekaran a kasar Amurka inda yake karban magunguna a dalilin raunuka da ya samu bayan hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi.

DUBA WANNAN: Shin ya Ayo Fayose da sauran masu bakar adawa zasu karbi dawowar shugaba Buhari?

A cewar wani daga cikin dangin marigayin, an garzaya da Babangida Suntai zuwa asibiti a Abuja tun makon da ya wuce domin yi masa magani amma a jiya da yamma ne likitoci suka bada sanarwan rasuwar tasa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel