Wani dan Nijeriya ya zana wata hoton jirgi dan nuna murnarsa na dawowar Shugaban kasa
Wani dab Nijeriya mai suna Abu Sulaiman ya bayyana wata hoton jirgi da ya zana a kan shafinsa na facebook,inda yake nuna farin cikinsa akan dawowar Shugaban kasa
Abu Sulaiman ya bayyana cewa ya ji dadi sosai da ya kasance daya daga cikin wayanda suka sami damar yin bikin dawowar shugaban kasa.Saboda haka ya zana wata hoton jirgin sama mai dauke da rubutu kaman haka,"NIGERIAN PRESIDENTIAL PLANE" jirgin shugaban Nijeriya.
KU KARANTA KUMA: Jihar Katsina, Daura sun yi murna da dawowar Buhari daga London
Yayi rubutu a shafinsa kaman haka:"Hotunan bikin jin dadi
Nayi farin ciki da kuma girmamawa sosai don kasance wa daya daga cikin wayanda suke murna dan dawowar shugaban kasar Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya, wanda ya yi kwana 103 a London dan samun kiwon lafiya".
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Dubi murnar dawowar Buhari
Asali: Legit.ng