Gawar tsohon gwamnan Taraba Suntai, ta isa Jalingo, ana shirin jana'izarsa
- Gawar marigayi gwamnan Taraba, Danbaba Suntai ta isa garin Jalingo
- Gawar ta iso filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja daga kasar Amurka
- Kusoshin gwamnatin jihar Taraba sun fito tarbar wannan gawa
Gawar marigayi tsohon gwamnan jihar Taraba, Danbaba Suntai ta iso babban birnin Jalingo na jihar ta Taraba.
An samu rahoton cewa, gawar ta iso kasa Najeriya daga kasar Amurka a ranar 18 ga watan Agusta, inda jirgin da ya dauko ta ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin karfe 5:00 na safiyar jiya.
Daga bisani gawar wadda ta iso garin Jalingo da misalin karfe 10:58 na safiyar yau Asabar, inda gwamnan jihar Taraba, Arch Darius Ishaku ya je tarbar ta a filin jirgin sama na Danbaba Danfulani Suntai kuma a ka garzaya da ita gidan shi domin a hadata zuwa makwancinta.
KU KARANTA: Shugaba Muhammadu Buhari zai dawo yau asabar – Femi Adesina
Matar marigayi Suntai, Hauwa'u Suntai, tana cikin wadanda suke je tarbar gawar a filin jirgin saman na Abuja.
Za a binne gawar Suntai a mahaifarsa ta Suntai ta karamar hukumar Bali a jihar ta Taraba
Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Bidiyo na gawar Suntai
Asali: Legit.ng