Ayi a gama: Real Madrid za ta kara gwabzawa da Barcelona

Ayi a gama: Real Madrid za ta kara gwabzawa da Barcelona

- Real Madrid za su kara fafatawa da Barcelona a yau

- Wanda yayi nasara zai lashe Gasar Super Copa na kasar

- A karon farko dai Real Madrid tayi nasara da ci 3-1

Za ku ji cewa dai yau za ayi ta ta kare tsakanin Kungiyar Real Madrid da abokan hamayyar su Barcelona a wajen cin kofin Super Cup.

Ayi a gama: Real Madrid za ta kara gwabzawa da Barcelona
Wa zai dauki Super Cup yau?

Dama an ce karo da karo sai rago. Real Madrid za ta kara gwabzawa ne da Barcelona a zagayen karshe na wasan cin kofin na Super Cup na Sifen. A wasan farko Madrid tayi nasara a gidan Barcelona da ci 3-1.

KU KARANNTA: Watakila Gola Buffon ya ci kyauta

Ayi a gama: Real Madrid za ta kara gwabzawa da Barcelona
Dan wasan Kungiyar Real Madrid Ronaldo

Real Madrid za ta buga babu gwarzon Dan wasan ta Ronaldo bayan ya sha jan kati a wasan da aka buga Ranar Lahadi wanda har ya tura Alkalin wasa. Dan wasa Asensio shi ma ya jefa kwallo a ranar bayan Dan wasan bayan Barcelona Pique ya ci ragar sa.

Kun ji cewa duk wanda yayi nasara a wasanni biyun da aka buga zai dauki Super Cup na kasar Sifen wanda ake gwabzawa tsakanin wanda ya ci Gasar La-liga da kuma wanda ya ci Gasar Copa Del-Rey.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Labarin mawakan Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel